Sojan Afghanistan ya kashe sojoji hudu

Image caption Dakarun sojin Jamus dake Afghanistan

Rundunar kasashen duniya dake Afghanistan ta fadawa BBC cewa, wani sojan Afghanistan sun kashe dakarunta hudu.

Wannan dai shi ne karon farko da aka kashe dakarun kasashen duniya a Afghanistan ta wannan hanya cikin fiye da wata guda.

A lardin Paktika na gabashin kasar dake kusa da iyaka da Pakistan an wani dake sanye da kakin sojan Afghanistan ne ya harbe sojan kasashen duniya uku.

A yammacin kasar kuma an kashe sojan kasashen duniya guda:

Wakilin BBC a kasar ya ce rundunar kawance ta kasashen duniya dake Afghanistan, wato ISAF ba ta fayyace kasashen da dakarun da aka kashe din suka fito ba, amma kuma yawancin dakarun dake aiki a yankin da lamarin ya auku Amurkawa ne.

Karin bayani