Mandela na asibiti tare da matarsa Graca

Image caption Nelson Mandela da Uwargidansa, Graca

Uwargidan Nelson Mandela, wato Graca Machel tana asibiti tare da shi, inda yake jinyar cutar huhu da ya sha fama da ita.

Tare da ita aka kai shi asibitin da ba a bayyana sunansa ba a birnin Pretoria da asubahin yau Asabar.

Yanzu dai Nelson Mandela, wanda dan shekaru casa'in da hudu ne yana numfashi da kansa.

Ana kallon Mandela a matsayin uban kasa wanda ya jagoranci sauyin mulki a cikin kasar daga wajen tsiraru farar fata don komawa tafarkin mulkin demokradiyya.

Wata sanarwa data fito daga fadar shugaban Afrika ta Kudu dai ta bayyana cewar likitoci na iyaka kokarinsu don ganin cewar ya samu lafiya.

Mista Mandela ya kamu da tarin fuka ne lokacin daya shafe shekaru 27 a kurkuku yana jagorantar yaki da mulkin danniya na turawan mulkin mallaka.

Wannan ne karo na uku a bana da aka kwantar da Mista Mandela a asibiti.

Karin bayani