Sudan zata katse man Sudan ta kudu

Image caption Wani wurin haƙar mai

Gidan rediyon gwamnatin Sudan yace, shugaba Omar Al Bashir ya bada umarnin dakatar da kai mai zuwa kasuwannin duniya daga bututan da suka fito daga Sudan ta kudu suka ratsa ta cikin Sudan.

Sudan ta kudu wacce kasa ce da ba ta da gaɓa ta ruwa, a bara ta dakatar da fitar da hakar manta bayan an samu takaddama akan ko nawa ya kamata ta rika biyan Sudan saboda kai manta zuwa tashoshin jiragen ruwa.

Cikin watan jiya ne dai shugaba Omar Al Bashir yayi barazanar katse fitar da man Sudan ta kudu ta cikin kasarsa, idan har bata daina goyon bayan 'yan tawaye ba.