An soki Amurka a kan tatsar bayanai

Image caption Tim Berners-Lee ya ce matakin ya sabawa tsarin dimokaradiyya

Mutumin da ya kirkiro tsarin sadarwa na intanet, watau World Wide Web, Tim Berners-Lee, ya mayar da martani cikin fushi game da matakin da Amurka ta dauka na bibiyar bayanan mutane ta hanyar intanet da wayoyin sadarwa.

Sir Tim Berners-Lee ya ce hakan ya sabawa ginshikan mulkin dimokaradiyya da suka bai wa kowa damar gudanar da lamuransa cikin sirri, yana mai cewa matakin zai yi mummunar illa ga mulkin dimokaradiyya.

Su ma mutanen da suka mallaki shafukan google da facebook, Larry Page da Mark Zukerberg, sun musanta cewa Amurka na bibiyar bayanan mutane ta shafukan nasu.

Tun da farko dai Shugaba Obama ya ce sun dauki matakin ne domin kare kasar daga sake abkawa hannun 'yan ta'adda.

A cewarsa majalisar dokokin kasar ta amince da matakin.

Karin bayani