An tattauna tsakanin Korea ta arewa da ta kudu

Image caption Masu tattauna daga kasashen Kore ta arewa da ta kudu

Jami'an gwamnatocin ƙasashen Korea ta arewa da ta kudu sun yi tattaunawar farko cikin shekaru biyu, yayin da cikin watanni biyun da suka gabata ake samun sararawar zaman ɗar-ɗar tsakanin ƙasashen biyu.

Jami'an gwamnatin Korea ta kudu sun ce, tattaunawar ta gudana cikin tsanaki, kuma suka ce, yanzu suna ƙoƙari ne su sanya lokacin yin wani taron a mataki na gaba cikin makonnin dake tafe a birnin Seoul.

Wannan dai shi ne zai zama karon farko cikin shekaru shida da ministoci daga kasashen biyu zasu gana kai tsaye.

Korea ta arewa ta bada shawarar tattaunawa da Korea ta kudun akan batutuwan haɗin gwiwa tsakaninsu da suka haɗa da batun, sake buɗe masana'antar nan da aka rufe cikin watan jiya.