Benghazi:Hasfan sojin Libya ya yi murabus

Image caption Yussef al Mangoush

Babban hafsan sojan kasar Libya zai sauka daga kan mukaminsa bayan majalisar dokokin kasar ta amince da murabus dinsa.

Wannan sanarwa dai na zuwa ne bayan an baiwa rundunar sojan kasar umarnin ta karbe iko da dukkan sansanonin da sojan sa-kai ke gudanarwa a birnin Benghazi.

A wani taro cikin sirri ne, Janar Yussef al-Mangoush ya mika takardarsa ta ajiye aiki, inda majalisar take ta amince kuma take kokarin nada wanda zai maye gurbinsa.

A jiya Asabar ne, fada ya barke a birnin Bengazi a kusada shalkwatar wata kungiyar tsageru masu rike da makamai mai suna Libya Shield Brigade, bayan da masu zanga-zanga suka bukaci, a tarwatsa kungiyar tsagerun wacce ke kunshe da tsaffin dakarun 'yan tawaye.

Gwamnatin tarayyar Libya dai ta gaza samarda tsaro a fadin kasar saboda yawaitar makamai tsakanin al'umma.

A wannan tashin hankalin dai, akalla mutane 30 ne suka gamu da ajalinsu yayinda wasu kusan dari suka samu raunuku.

Karin bayani