Mandela ya yi kwanaki biyu a asibiti

Image caption Desmond Tutu ya yi kira a yi wa Mandela addu'a

Tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu, Nelson Mandela, ya shafe dare na biyu a asibitin da ke birnin Pretoria inda ake duba lafiyarsa sakamakon cutar huhu da ke damunsa.

Jami'ai sun ce Mista Mandela, mai shekaru casa'in da hudu a duniya, yana yin numfashi ba tare da samun taimako ba.

Sai dai har yanzu yana cikin mummunan hali, kodayake ana tsammani yanayin da yake ciki ba zai dagule ba.

Babban abokinsa, Archbishop Desmond Tutu, ya yi kira ga 'yan kasar su yi wa Mista Mandela adduo'in samun lafiya.

Shugaba Jacob Zuma ya bayyana cewa zai kai wa tsohon shugaban ziyara da zarar ya samu amincewar yin hakan daga wajen likitoci.

Iyalinsa suna tare da shi

Iyalinsa sun kasance tare da shi bayan likitoci sun yanke shawarar dauke shi daga gidansa da ke Johannesburg zuwa asibiti lokacin da jikinsa ya yi zafi.

Yanayin lafiyar Mista Mandela, wanda ake kallo a matsayin uban kasa, ya sanya jikin mutane ya yi sanyi.

Wannan shi ne karo na uku da ake kwantar da shi a asibiti cikin watanni shida.

Nelson Mandela ya yi fama da cutar numoniya a watan Maris, kuma ya kwashe shekaru da dama yana fama da cutar huhu .

Karin bayani