Senegal ta lashe kokawar gargajiya

Shugaban Senegal Macky Sall
Image caption Senegal ta yi wa kasashe zarra

Kasar Senegal ta yi nasara a gasar kokawar gargajiyar da aka kammala tsakanin kasashen kungiyar ECOWAS a kasar Nijar.

'Yan kokawar Senegal sun ci lambar zinariya da tukwici na kudi miliyan biyar na cfa.

Nijar ce ta zo ta biyu inda ta samu kyautar lambar azurfa da kudi cfa miliyan uku.

Kazalika, Najeriya ce ta zo ta uku, kuma an ba ta kyautar tagulla da cfa miliyan daya da rabi.

Kasashe 14 daga cikin 15 na kungiyar ta ECOWAS ne dai suka halarci Gasar kokawar.

Karin bayani