A shirye muke mu hau teburi —Abdu Labo

Tutar Jamhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jamhuriyar Nijar

A Jamhuriyar Nijar, bangaren Alhaji Abdu Labo na jam’iyyar CDS Rahama ya ce a shirye yake ya zauna teburi guda da bangaren Alhaji Mahaman Usman domin soma tunanin yadda za su farfado da jam'iyyar.

Hakan dai ya biyo bayan hukuncin da Kotun Kolin kasar ta yanke ne, wanda ya rushe taron Congres din da bangaren na Mahaman Usman ya shirya a Damagaram.

A cewar Alhaji Labo, “…Rikici ya kare. Ke nan sai mu komo, mu zauna, mu sake salo, mu ta da [jam’iyyarmu] tun da kun ga shekara biyu da wata hudu ana cikin jaye-jaye; to Allah Ya kawo mana saukin wannan abin ya kamata mu karbe shi da hannu biyu”.

Dangane da wanda zai fara yunkurin tuntuba a tsakanin bangarorin biyu kuwa, cewa ya yi: “Tuntuba, duk wanda ya yi ta—kuma dole ne a yi ta—suna iya kiranmu, muna iya kiransu; wannan ina jin karamin aiki ne”.

Karin bayani