Zaman dar-dar na neman dawowa a Sudan

Sudan ta Kudu ta ce za ta gabatar da korafi a hukumance ga Majalisar Dinkin Duniya a game da kutsen sojojin Sudan a cikin kasarta.

Ministan yada labarai na Sudan ta ta Kudu Barnaba Marial Benjamin yace sojojin Sudan su ja daga a wasu yankuna na jihar Upper Nile inda sojojin sojin Sudan ta Kudu suka janye a karkashin wani shirin yarjejeniya da aka cimma.

Ya ce za su gabatar da korafinsu ga sojojin Habasha wadanda ke cikin rundunar sa ido ta Majalisar Dinkin Duniya dake sinturi akan iyakar da kuma rundunar hadaka.

Cikin wata hira da BBC ya ce zasu gabatar da kukansu ga dakarun Ethiopia dake aiki karkashin Majalisar Dinkin Duniya.