China ta kaddamar da kumbon sama jannati

China, Space, Mission
Image caption Jirgin sama jannati

Kasar China ta kaddamar da sabon shirinta zuwa sararin samaniya ta hanyar amfani da kumbon Shenzhou-10.

'Yan sama jannati uku sun bar sansanin Jiuquan da ke yankin Mongolia a kumbon samfurin March 2F.

Jagoransu, Nie Haisheng da mukarraban sa, Zhang Xiaoguang da kuma Wang Yaping sun shirya shafe kimanin makonni biyu ne a dakin gwaje-gwajen da ke tashar Tiangon a sararin samaniya.

Wang ta kasance mace ta biyu 'yar sama jannati a China, sannan zata kasanace 'yar kasar ta farko da za ta koyar da dalibai kan ilmin sararin samaniya daga tashar ta sama jannati da ke Tiangong.

Kwanson da ke dauke da 'yan sama jannatin ya rabu da rokar da aka harba shi da shi ne mintuna 9 bayan an harba shi, abinda ya janyo tafi daga masu kula da tashar da ke kasa.

Tashar talbijin din China ta hasko hotunan shugaba Xi Jinping yana yiwa 'yan sama jannatin fatan alkhairi.

" Ya ce kun sanya al'ummar China na alfahari da mu", Shugaban ya shaidawa Nie da mukarraban sa cewa, kun samu horo sannan kuma kun shirya kan ku, dan haka bana jin ko dar a aikin da zaku gabatar, "ina yi muku fatan alkhairi da kuma jimirin dawowar ku cikin nasara."

Karin bayani