'Yan Africa ta Kudu na yiwa Mandela addu'o'i

Nelson Mandela
Image caption Nelson Mandela

Shugaban Africa ta Kudu, Jacob Zuma ya ce baki dayan Africa ta Kudu na yiwa Nelson Mandela addu'ar ya samu sauki cikin gaggawa.

Tsohon shugaban na Africa ta kudu ya na kwance a asibiti a sashen wadanda suke cikin matsanancin hali a wani asibiti a Pretoria, inda ake yi masa maganin cutar huhu.

A jawabinsa na baya bayan nan, Mr Zuma, ya bayyana Mandela a matsayin mutum mai juriya da karfin hali, inda ya kara da cewar yana da karfin guiwar cewa likitocin da ke yiwa Mandela magani suna aiki tukuru.

An kwantar da Mr Mandela a asibiti ne ranar asabar kuma dukkanin zuru'arsa sun kai masa ziyara haka nan kuma an tsaurara matakan tsaro a asibitin.