Snowden: Amurka ta ki bayyana matsayinta

Edward Snowden
Image caption Edward Snowden ya ce tatsar bayanan na barazana ga dimokuradiyyar Amurka

Har yanzu Fadar Gwamnatin Amurka ta White House ta ki ta ce komai a kan ko za ta bukaci a taso keyar Edward Snowden, mutumin da ya bankada bayanan sirrin shirin Amurka na tatsar bayanai.

Abin da kakakin Fadar, Jay Carney, ya fada kawai shi ne an kaddamar da bincike, sannan ya jaddada bayanin da gwamnatin ta sha yi cewa Snowden ya yi illa ga harkar tsaron Amurka.

Wani tsohon mai baiwa hukumar tsaron kasa shawara ta fuskar shari’a, Stewart Baker, ya ce lallai ne a hukunta Mista Snowden:

“Abin da ya aikata yiwa dokokin Amurka karan-tsaye ne; kuma dagawa ce ta innanaha. Kamar yana cewa ne ‘ga abin da dokokin Amurka suka tanada amma bai dace da abin da ni nake ganin ya kamata su tanada ba, don haka zan bankada sirrin duk kuwa da illar da yin hakan ka iya jawowa’.

“Saboda haka wannan laifi ne da ya wajaba a yi masa hukunci saboda aikata shi”.

Sai dai yayin da wadansu ke yiwa Mista Snowden kallon fandararre, wadansu kuwa kallon jarumi suke yi masa.

Dubun dubatar mutane na ta rattaba hannu a kan wata takardar koke da aka lika a shafin intanet na Fadar White House mai dauke da kiran a yi masa afuwa nan take.

Daya daga cikin ’yan jaridar da aka kwarmatawa bayanan na sirri, Ewen MacAskill, ya ce nauyin alhakin da ya rataya a wuyansa ne ya sa Mista Snowden ya aikata abin da ya aikata.

A cewarsa, “[Snowden] ya yi shekaru akalla biyar yana tunani a kan wannan al'amari, kuma ya san abin da zai biyo baya”.

Mista MacAskill ya kara da cewa, “Ya san cewa yana iya fuskantar daurin rai-da-rai, amma ya ji a ransa cewa dole ne ya bankada wannan al'amari ko da kuwa daga yanzu rayuwarsa za ta kasance cikin kunci”.

Ko ma dai mecece makomar Mista Snowden, hukumomin leken asiri na Amurka za su fuskanci matsin lamba su sake nazari a kan hanyoyin gudanar da ayyukansu.

Musamman wani batu da suke bukatar su warware shi ne ko yawan mutanen da ake dankawa amanar bayanan sirri ya wuce kima.

A halin da ake ciki dai Mista Snowden ya yi batan dabo daga otal din ya sauka a Hong Kong.

Ya shaidawa 'yan jarida cewa kudinsa ya kare kuma yana sa ran hukumomin leken asiri na Amurka za su shiga farautarsa.

Dan shekara 29 a duniya, tsohon ma'aikacin na hukumar liken asiri ta CIA ya ce ya kwarmata bayanan shirin na sa ido a kan miliyoyin bayanan da ake musayarsu ta wayar salula da sakwannin email da sauran hanyoyi ne saboda shirin na barazana ga dimokuradiyyar Amurka.

Karin bayani