G8 ta koka kan yadda cutuka ke bijire ma magungunan Antibiotics

Magungunan antibiotics da cutuka ke bijire ma
Image caption Magungunan antibiotics da cutuka ke bijire ma

Ministocin kimiyya daga kasashen kungiyar G8 masu cigaban masana'antu na ganawa a nan London domin tattauna karuwar matsalar bujirewar da magungunan kashe kwayoyin cuta na Antibiotics ke yi.

Kwararrun masana sun ce amfani da maganin na Antibiotics fiye da kima shi yake kara haddasa karuwar matsalar wanda ke sanya maganin bujirewa.

Dr Aminu Musa, malami a sashen kimiyyar harhada magunguna a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria , ya ce wannan babbar matsala ce, kuma daya daga cikin dalilan dake haddasa ta shi ne yadda wasu ke fara shan magunguna, amma da sun ji sauki , sai su daina sha ba tare da sun kammala shan maganin kamar yadda likita ya umurce su ba.

Haka nan ya ce akwai matsalar kuma zuwa sayen magunguna ba tare da izinin likita ba.

A yanzu dai babban kalubale shi ne samar da sabbin magungunan na Antibiotics, da kuma matakan da gwamnatoci zasu dauka na rage komawa gidan jiya.