Ana ci-da-gumin yara miliyan 10 —ILO

Tambarin ILO
Image caption Kungiyar ILO ta ce miliyoyin yara na aiki a karkashin yanayi mai kama da bauta

Kungiyar kwadago ta duniya, ILO, ta ce miliyoyin yara ne a fadin duniya ke ayyukan gida a yanayin da sau da dama ke cike da hadari a wadansu lokutan ma har ya kan zama tamkar bauta.

A rahoton da ta fitar na Ranar Yaki da Ci-da-Gumin Yaran, kungiyar ta bukaci a samar da dokokin da za su kawo karshen ta'adar.

Kungiyar ta ILO ta yi kiyasin cewa yara miliyan goma da dubu dari biyar ’yan kasa da shekaru 14—wadanda galibi mata ne—na kashe rana a kullum wajen ayyukan goge-goge, da girke-girke, da debo ruwa, da kuma kula da tsofaffi da kananan yara.

Kuma da yawa daga cikinsu ba a biyansu ba kuma a ba su damar zuwa makaranta.

Rahoton ya kara da cewa wadansu daga cikinsu ana safararsu ne inda suke shiga hadarin cin zalinsu da kuma badala.

Karin bayani