Jonathan ya koka da tsarin 'yan sanda

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya bayyana cewa wata matsalar da ke damun rundunar 'yan sanda kasar ita ce yin karin mukami ga jami'an da ba su cancanta ba.

Shugaban ya ce wannan matsalar na daga cikin dalilan suka sa jam'an 'yan sanda ba sa tabuka abin kirki a aikinsu.

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya lura cewa ba a bin wasu ka'idoji na musamman da za su sanya wa 'yan sanda kaimi wajen yi musu karin girma, kuma wannan ne ya sa jami'an 'yan sanda da dama sun samu kansu a muhimman mukamai ba tare da cancanta ba.

Kuma wannan ne ya sa irin mukaman da suke rike da su ba sa wani tasiri a kan ayyukansu ta fuskar kwazo ko kwarewa.