Zanga-zanga ta ɗan lafa a Turkiya

Image caption Wani yana jefa wuta a dandalin Taksim

An dan sami lafawar al'amura a tsakiyar birnin Santabul bayan da aka shafe tsawon daren ranar Talata ana artabu a yunkurin da 'yan sandan kwantar da tarzoma ke yi na tarwatsa masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Dambarwa ta yi sauki a dandalin Taksim inda nan ne 'yan zanga-zangar suka yi zaman dirshan, sai dai kuma wasu daga cikin su na taruwa gungu-gungu a daura da wurin shakatawa na Gezi wanda sakamakon shawarar gwamnati na yin wasu aikace-aikace a wurin ne ya haddasa zanga-zangar da ta rikide ta kuma yadu a fadin kasar.

Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle, ya baiyana matakin da 'yan sandan da cewa tamkar wani sako ne mara kan gado Turkiya ke aikewa a cikin gida da waje.

Sai dai kuma gwamnan Santanbul Huseyin Avni Mutiu, ya ce 'yan sanda za su cigaba da daukar wannan mataki har sai sun fatattaki masu zanga zangar daga dandalin na Taksim.

Karin bayani