Iran na muzgunawa ma'aikatanmu! BBC

BBC ta ce hukumomin Iran sun yi barazana ga yanjaridar dake aiki a sashen harshen Farsi na BBC dake London, yayinda kasar take shirin gudanar da zaben Shugaban kasa ranar Juma'a.

BBCn ta ce ma'aikatar leken asirin a Tehran ta kira dangin ma'aikata akalla 15 dake aiki a sashen harshen Farisa na BBCn a nan London inda ta sheda masu dole ne yan uwansu su daina yiwa BBC aiki ko kuma rayuwarsu na cikin hadari.

Su kansu dangin ma'aikatan an gargade su cewar za su iya rasa ayyukansu.

BBC ta ce ta damu matuka da abinda ta kira wannan musgunawa da ba a taba ganin irinta ba.