Najeriya: An kai hari a ƙauyen Kwasa-Kwasa

Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya da asubahin yau ne gungun wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan fashi ne suka kashe akalla mutane biyar a kauyen Kwasa-Kwasa dake karamar hukumar Birnin Gwari dake jihar Kaduna.

Koda a karshen mako dai wasu 'yan bindiga sun kai hari a wasu kauyuka biyu na biyu a karamar hukumar Birnin Gwari inda suka kashe mutane akalla mutane bakwai.

Malam Adamu Sarkin Noma, daya ne daga cikin shugabannin 'yan sintiri a yankin karamar hukumar Birnin Gwarin.

Cikin 'yan watannin nan dai ƙaramar hukumar Birnin Gwari na fama da hare-haren 'yan fashi da suke haddasa asarar rayuka.