Makamai: Za'a cigaba da tsare kwarori

Mutum-mutumin Kotu
Image caption Mutum-mutumin Kotu

Wata babbar Kotu a Abuja ta ba da umarnin cigaba da tsare kwarori uku da ake zargi da shigar da makamai Najeriya ba bisa ka'ida ba.

Kwarori uku da ake zargi sun bayyana a gaban kotun, a karar da suka shigar da hukumomin Najeriyar, game da cigaba da tsare su ba bisa ka'ida ba.

Hukumar ta gurfanar da kwarorin ne a ranar Alhamis, bayan umarnin da kotun ta bayar na cewa, hukumar ta gurfanar da su a gabanta.

Kwarorin sun nemi a biyasu diyyar naira biliyan hamsin, saboda tsare su da aka yi na wani lokaci ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ba.

Haka kuma sun yi zargin cewa hukumar tsaro ta SSS ta ki ta basu damar ganawa da lauyoyinsu.

Sai dai a nata bangaren, hukumar tsaro ta farin kaya, SSS na zargin 'yan kasar ta Lebanon da alaka da kungiyar masu gwagwarmaya ta Hezbullah tare da shigar da makamai kasar ba bisa kaida ba.

Kuma ta ce tana da kwakkwarar hujja game da tuhumar da ake yi wa kwarorin na aikata ta'adanci a kasar.

Ta kuma ce binciken da ake yi yanzu ya dauki wani sabon sallo, saboda abu ne da ya shafi kasashen duniya.

Hukumar ta kuma kara da cewa, idan aka saki wadanda ake zargin cikin gaggawa, watakila hakan ya shafi makomar shari'ar kasancewar daya daga cikin mutanen da ake tuhumar har yanzu ana nemansa ruwa a jallo.

Alkalin kotun ya umurci hukumar SSS din da ta cigaba da tsare 'yan kasar Lebanon din uku.

Sannan Mai shari'a Adeniyi Ademola ya umarci hukumar ta tabbatar ta gurfanar da kwarorin, a duk zaman da za ta yi, ta kuma basu damar ganawa da lauyoyinsu.

Alkalin ya sa ranar 21 ga watan Yuni, a matsayin ranar da kotun za ta cigaba da saurarar shari'ar.

Makamai

Gwamnatin Najeriyar dai na zargin 'yan kasar Lebanon din uku da shigar da makamai cikin kasar ba bisa kaida, bayan ta gano wasu muggan makamai a gidan daya daga cikin Kwarorin dake jihar Kano.

Hakan ya kai hukumar SSS ga rufe wani shagon sayar da kayyaki mai suna Amigo dake Abuja, da kuma wani wajen shakatawa da ake kira Wonderland, mallakar wasu daga cikin kwarorin da ake tsare da su.

A makon da ya gabata ne kuma aka gurfanar da kwarorin a gaban wata kotun Majistare dake birnin Abuja, a wata shari'ar ta daban, wadda gwamnatin Najeriyar ta shigar.