'Yan majalisun Najeriya sun yi sabani

Kakakin Majalisar Wakilai ta Najeriya, Aminu Waziri Tambuwal
Image caption Majalisar Wakilai ta Najeriya ta dauki matsayin da ya saba da na Majalisar Dattawa

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta dauki matsayin da ya yi hannun-riga da na Majalisar dattawa dangane da wadansu gyare-gyaren da ake kokarin yi ga kundin tsarin mulkin kasar, musamman ma batun wa’adin mulki ga shugaban kasa ko gwamnoni.

Ita dai Majalisar ta Wakilai matsayinta shi ne a bar wa’adin mulkin yadda yake, wato shekaru hudu sau biyu.

A cewar Honourable Ibrahim Tukur Elsudi, mamba a Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Majalisar, “ra’ayin mazabunmu shi ne a bar wa’adin yadda yake”.

Dan Majalisar ya kara da cewa dalilan da jama’a suka ba su wanda ya kai ga daukar wannan matsayi shi ne cewa idan masu rike da mukamai suka san ba za su sake neman zabe ba, to ba za su tsaya su yi aiki yadda ya kamata ba.

“Amma ka ga idan aka yi wa’adi na shekara hurhudu sau biyu”, inji Honourable Elsudi, “a wa’adi na farko, yawanci za ka ga wadanda aka zabe su a tsorace suke—za su yi aiki gadan-gadan don a yaba musu, [kuma] su tabbatar da cewa an sake zabensu”.

Ya kuma ce dalilin da ya sa matsayinsu ya bambanta da na Majalisar Dattawa—duk da cewa ita ma Majalisar Dattawan na cewa matsayinta ra’ayin al’ummar da mambobinta ke wakilta ne—shi ne bambanci a yadda suka bullowa al’amarin: “Tsakani da Allah duk wanda ke bin abubuwan da muke yi a Majalisar [Wakilai] zai fahimci cewa dukkanmu—ko wanne dan majalisa—ya koma mazabarsa; mafi rinjaye su suka yarda da haka.

“Su kuma ‘yan Majalisar Dattawa, sun zauna ne shiyya-shiyya, ba [a] mazabunsu suka zauna ba…. Da sun kusanci jama’a, ina ba ka tabbacin cewa wannan matsaya da suka dauka da ba ta kasance haka ba”.

Karin bayani