Za a yi kuri'ar raba-gardama a Turkiyya

'Yan sandan Turkiyya
Image caption 'Yan sandan Turkiyya bayan sun yi arangama da mau zanga-zanga a birnin Ankara

Wani babban jami'in jam'iyyar AKP mai mulki a Turkiyya ya ce za a gudanar da kuri'ar raba-gardama a kan makomar Dandalin Shakatawa na Gezi da ke birnin Santanbul.

Batun sake fasalin dandalin ne ya harzuka zanga-zangar da ta barke makwanni biyu da suka gabata bayan 'yan rajin kare muhalli sun bayyana adawarsu da shirin.

Tayin gudanar da kuri'ar raba-gardamar dai ya biyo bayan wata tattaunawa ce tsakanin Firayim Minista Recep Tayyip Erdogan da masu fafutukar a yunkurin kawo karshen tarzomar.

Da yake jawabi ga wani taron manema labarai, mataimakin shugaban jam'iyyar kuma kakakinta wanda ya sanar da shirin gudanar da kuri'ar, Husayn Celik, ya kuma yi kira ga masu zanga-zangar da su kauracewa dandalin.

“Ina kira ga wadanda suka je dandalin don kawai su bayar da kariya ga muhalli ko don su bayyana ra’ayoyinsu; tun da yanzu mun yanke shawarar gudanar da kuri’ar raba-gardama, ya kamata ku bar Dandalin Shakatawa na Gezi ba tare da bata lokaci ba, saboda komai ya koma yadda yake a da kuma mutanen da ke son zuwa dandalin su samu damar yin hakan cikin kwanciyar hankali”, inji shi.

Mista Celik ya kuma yi gargadin cewa duk wanda ya zabi ya ci gaba da zama a dandalin ko ya tayar da zaune tsaye to zai gamu da fushin ’yan sanda.

Wannan ne dai karo na farko da jam’iyyar ta bayyana yiwuwar baiwa masu kada kuri’a wuka-da-nama wajen yanke shawara a kan makomar dandalin.

A halin da ake ciki kuma, ’yan sandan kwantar da tarzoma a babban birnin kasar, Ankara, sun harba hayaki mai sa hawaye da nufin tarwatsa masu zanga-zanga wadanda ke zargin Mista Erdogan da yunkurin kakaba akidunsa na Musulunci a kan kasar wacce ke bin tafarkin raba addini da siyasa.

Tun da farko dai gidan talabijin na kasar ya ambato Mista Erdogan yana shaidawa wani taron ’yan kasuwa cewa zanga-zangar za ta zo karshe a cikin sa’o’i ashirin da hudu.

Karin bayani