An tsayar da ranar zabe a Zimbabwe

Image caption Shugaba Robert Mugabe

Wata takaddamar siyasa ta barke a Zimbabwe bayan da Shugaba Robert Mugabe ya fitar da wata doka dake cewar za a gudanar da zabe a ranar 31 ga watan Yuli.

Nan da nan Pirayim Minista, Morgan Tsvangarai, ya ce Shugaban kasar na bi ta bayan majalisar dokoki, kuma zai nemi ya toshe yunkurin.

A wajen wani taron manema labarai, ya zargi Mr Mugabe da keta sharuddan yarjejeniyar raba ikon da aka amince kansu shekaru 5 da suka wuce bayan zabe mai cike da tashin hankali da takaddama.

Mr Tsvangarai ya bukaci cewar a jinkirta gudanar da zaben har an gudanar da sauye sauye don tabbatar da zaben gaskiya da adalci.

Karin bayani