Mandela yana samun sauƙi, inji jikansa

Image caption Nelson Mandela, yana kwance a asibiti

Mandla Mandela, wanda jika ne ga Nelson Mandela yace, kakansa yana samun sauƙi a asibiti, inda yanzu ya kwashe mako guda yana jinyar cutar huhu dake sha fama da ita.

Wadannan kalamai na jikan na Nelson Mandela sun yi daidai da sanarwar baya-bayan nan da gwamantin Afurka ta kudu ta fitar, tana cewa, dattijin da ake matukar girmamawa, yana cikin wani hali, amma fa yana samun sauki.

Yanzu dai Nelson Mandela, mai shekaru casa'in da hudu ya shafe mako guda kenan a asibiti a Pretoria, hakan tasa wasu suna nuna damuwa akan halin da yake ciki.