An kawar da cutar Tundurmi a Pilato da Nassarawa

Image caption Wani mai cutar Tundurmi

Cibiyar Carter ta bayyana cewar an kawar da wata mummunar cutar da ke haddasa mummunan kunburi kafafuwa daga wasu jihohi 2 na tsakiyar Najeriya, abinda ya sa aka ceci mutane miliyan 4 wadanda ke cikin hadarin kamuwa da ita.

Cutar ta Tundurmi, sauro ne ke haddasa ta.

Cibiyar ta Carter ta yi aiki tare da gwamnatin Najeriya da kuma kamfanonin harhada magani na duniya domin kawar da cutar.

Shirin mai cike da nasara za a fadada shi a cikin Najeriya -- kuma za a iya amfani da shi a sauran sasan duniya da suka hada da India da Indonesia a inda ciwon na Tundurmi yake wata annoba.