Al'ummar duniya za ta kai biliyan 10 nan da 2100

Dandazon jama'a
Image caption Al'ummar duniya za ta kai kimanin biliyan 10 nan da 2100

Wani sabon rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce India za ta iya wuce kasar China a matsayin kasar da ta fi kowacce yawan al'umma daga nan zuwa shekara ta 2028.

Sannan kuma rahoton ya ce Najeriya za ta fi Amurka yawan al'umma daga nan zuwa shekara ta 2050.

A cewar rahoton, yawan al'ummar duniya zai dinga karuwa cikin hanzari fiye da yadda ake zato.

Yawanci kuma daga kasashe masu tasowa za a samu karin yawan al'ummar, musamman ma a kasashen Afrika.

yawan al'ummar duniya zai dinga karuwa cikin hanzari fiye da yadda ake zato.

Rahoton ya cigaba da cewa, rabin karuwar jama'ar da za a samu tsakanin shekarar 2013 da dubu biyu da dari daya za su fito ne daga kasashen takwas da suka hadar da, Najeriya da India da Tanzania da Jamhuriyar dimokradiyyar Congo da Nijar da uganda da Ethiopia da kuma Amurka.

Rahoton ya kuma gano cewar, akwai yiwuwar al'ummar Najeriya za ta iya dara ta Amurka yawa kafin shekarar 2050.

A yanzu dai yawan al'ummar Amurkan ya kai miliyan dari uku.

Yayinda al'ummar Turai kuma zai ragu ne da kashi goma sha hudu cikin dari a tsakanin shekarun 2013 da kuma 2100.

A sakamakon haka, ana kyautata zaton cewar, yawan al'ummar duniya baki daya zai iya kaiwa kusan biliyan goma nan da shekarar dubu biyu da dari, idan aka kwatanta da biliyan bakwai da miliyan dari biyu a yanzu.

Manyan kasashen duniya biyu wato China da India, sun rage yawan haihuwa, sai dai kuma a bangaren India har yanzu ana samun karuwar yawan al'umma, domin al'ummar kasar na da nisan kwana. Hakan dai na nuna cewa, da alama India zata iya zarta China a yawan al'umma nan da shekarar 2028, lokacin da yawan al'ummar kasashen biyu zai kai kimanin biliyan daya da miliyan arba'in da biyar.

Karin bayani