'An yi amfani da makami mai guba a Syria'

Ma'aikatan agaji a Syria
Image caption Amurka ta ce tabbatattun hujjoji sun nuna cewa an yi amfani da makamai masu guba a Syria

Amurka ta ce ta samu kwakkwarar hujjar da ke nuni da cewa gwamnatin Syria ta yi amfani da makamai masu guba a kan ’yan tawaye—ciki har da gubar nan ta sarin mai lahanta laka.

Fadar gwamnatin Amurkar ta White House ta ce a sanadiyyar hakan an hallaka mutane tsakanin dari da dari da hamsin.

A wata sanrwa da ta fitar, gwamnatin Shugaba Obama ta ce amfani da makamai masu guba ya saba da dokokin kasa-da-kasa.

Da ma dai gwamnatin kasar ta Amurka ta ce idan aka samu tabbatattun hujjojin amfani da makamai masu guba, to hakan na nufin Shugaba Bashar Al-Assad ya ketare wata iyaka da za ta tilasta mata sauya matsayi.

A cewar kasar ta Amurka, binciken cibiyoyinta na leken asiri ya tabbatar da cewa an yi amfani da makaman.

Sanarwar, wacce ta fito daga mataimakin mai baiwa Shugaba Obama shawara a kan al’amuran tsaro, Ben Rhodes, ta kuma ce: “Sakamakon samun hujja mai karfi cewa an yi amfani da makamai masu guba a kan al’ummar Syria, Shugaba Obama ya amince da fadada taimakon da muke baiwa Majalisar Koli ta Sojin ’yan tawaye”.

Sai dai sanrawar ba ta yi cikakken bayani a kan irin taimakon sojin da Amurka za ta baiwa ’yan tawayen ba.

“A takaice”, inji sanarwar, “ya kamata gwamnatin Assad ta ce san cewa ayyukanta ne suka kai mu ga kara yawa da fadin taimakon da muke baiwa ’yan adawa, ciki har da tallafi na kai-tsaye ga Majalisar Sojin—kuma za a ci gaba da kari a kan wannan yunkuri daga yanzu”.

Wannan dai muhimmin sauyin shawara ce a matsayin gwamnatin kasar ta Amurka, kuma karin kwarin gwiwa ga ’yan tawaye wadanda suka samu koma-baya a fafatawar da suke yi da dakarun gwamnati—wadanda ke samun taimakon dakarun Hezbollah—a ’yan kwanakin nan.

Karin bayani