Kungiyar Hezbollah zata ci gaba da tallafawa Syria

Magoya bayan Hassan Nasrallah
Image caption Kungiyar Hezbollah na goyan bayan dakarun Syria

Jagoran Kungiyar 'yan shi'a ta Hezbollah Hassan Nasrallah, yace mayakan kungiyar zasu cigaba da goyawa dakarun Shugaba Asad baya.

Ya shaidawa magoya bayansu a wani faifan bidiyo cewa za' a kai mayakan Hezbollah a duk inda ake bukatar su.

An dai yi imanin cewa kungiyar ta taka mahimmiyar rawa wajen murkushe 'yan tawaye a farkon watan da ake ciki a garin Qusair na Syria.

Tunda farko dai Babban Sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon yace baiwa kowanne bangare makamai ba zai kawo karshen halin da ake ciki ba.

Karin bayani