Iran: Rouhani ya lashe zaɓen shugaban ƙasa

Image caption Hassan Rouhani, wanda ya lashe zaben shugabancin Iran

Mai matsakacin ra'ayin rikau, Hassan Rouhani ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Iran yayin da ya lashe ƙuri'u miliyan takwas da rabi, kuma hakan ya ba shi sama kasan da kashi hamsin na ƙuri'un da aka kaɗa.

An dai samu fitowar masu kaɗa ƙuri'a sosai a zaben, inda aka ce kusan kashi saba'in da uku na masu rijista ne suka jefa ƙuri'a.

Magajin garin birnin Tehran, Mohammad Baqar Qalibaf shi ya zoma na biyu a zaɓen.

Tuni dai rahotanni ke cewa, jagoran addini na ƙasar, Ayatullah Ali Khamene'i ya taya Hassan Rouhani murnar nasarar da ya samu a zaɓen.