Turkiyya: 'Yan sanda sun aukawa masu zanga-zanga

A Turkiyya 'yan sandan sun aukawa masu zanga-zanga da suka mamaye dandalin Taksim da kuma dandalin Gezi dake tsakiyar birnin Santanbul bayan Praministan kasar, Recep Tayyip Erdogan ya sake yin kira ga masu zanga-zangar su maida wuƙar.

'Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka yi watsi da kiran da Praministan yayi cewa, zai janye shirinsa na gina rukunnan shaguna a dandalin biyu, idan suka kawo karshen zanga-zangar.

Yanzu haka dai an shiga ruɗani a dandalin Taksim.