An gargadi Mugabe kan zaban kasar

Shugabannin kasashen kudancin Afurka sun yi kira ga shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe ya jinkirta zaben da yace, sai anyi a karshen watan Yuli.

Shugabannin sun yi wannan kiran ne bayan wata ganawa da aka yi a Mozambique Robert Mugaben da kuma Praminista Morgan Tsavangirai, wanda tun farko yayi kiran a jinkirta yin zaben.

Zaben dai shi ne zai kawo karshen gwamnatin hadaka mai tanga-tangal da aka kafa tun bayan zaben da aka yi kasar mai cike da tashin hankali shekaru biyar da suka gabata.