Iraq: Bama-bamai sun kashe mutane 30

An samu fashewar bama-bamai da dama a garuruwa takwas na kasar Iraqi, kuma lamarin ya haddasa mutuwar mutane a kalla talatin.

Wannan tashin hankali dai yafi shafar kudancin Iraqin inda ba a saba ganin tashin hankali ba, inda aka samu fashewar bama-bamai a wasu manyan kasuwanni a Nasiriyah da kuma garin Basra.

A arewacin Iraqin dai an kai harin ne akan jami'an tsaro musamman ma garuruwan Mosul da kuma Sallahuddin.

'Yan sanda sun ce, an kai hari mafi muni ne a yankin Kut dake kusa da birnin Baghadaza, inda aka kai harin akan wasu leburori.