Zakir Naik ya kai ziyara Najeriya

Fitaccen malamin addinin musuluncin nan na India, Sheik Zakir Naik ya jaddawa musulmin Najeriya cewa, su kara fahimtar addininsu, kuma su iya zama da wadanda ba musulmi ba.

Malamin dai ya gudanar da wa'azi a Lagos ya, kuma kafin nan yayi wa'azi a Abuja, babban birnin Najeriya.

Musulim da ma wadanda ba musulmi ba da dama ne suka halarci wa'azin da malamin yayi yau a birnin Lagos.