Nelson Mandela na samun sauki

Shugaban kasar Afirka ta kudu, Jacob Zuma ya ce bayanan da ke fitowa daga bakin Likitoci na nuna cewa jikin tsohon shugaban kasar Nelson Mandela bai ci gaba da munana ba.

Mr Zuma ya bayyana hakan ne a lokacin wani jawabi na musamman da ya yi a ranar tunawa da wata arangama da wasu matasa bakar fata su ka yi a yakin da suke da wariyar launin fata a kasar a shekarar 1976 a garin Soweto.

Shugaba Jacob Zuna ya ce jikin Mr Mandela ba bu da di amma yana ci gaba da samun sauki, ya kuma bukaci jama'a da su ci gaba da yi masa addu'a.

Sama da mako guda kenan Mr Mandela ke jinya a wani Asibiti a Pretoria sakamakon cutar da yake fama da ita a huhu.