Birnin Agadez zai shiga sahun wuraren tarihi

Agadez za ta shiga sahun wuraren tarihi na duniya
Image caption Agadez za ta shiga sahun wuraren tarihi na duniya

Kwamitin kula da ilimi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO ya fara wani taro, domin nazarin wasu wuraren tarihi a kasashen duniya da za a sanya a sahun manyan wuraren adana tarihi na duniya.

Birnin Agadez na kasar Nijar na daga cikin wuraren da wannan kwamiti ke nazari a kai.

Farfesa Bube Namaiwa, masanin tarihi a jami'ar Sheikh Ante Diop dake kasar Senegal, ya ce shigar da Agadez da aka yi a sahun wadanda kwamitin zai duba abu ne da ya dace?

Birnin Agadez dai guri ne mai dumbin tarihi, inda ake da wani babban masallaci da ya kai sama da da shekaru 500, yayin da a can ne Shehu Usman Dan Fodio ya yi karatu a gaban Malam Jibril.

Karin bayani