India masu mutanen boye

Wasu mutane na rawa
Image caption Mutanen kauyen na amfani da rawa a wani bangare na bautarsu.

A wasu kauyukan India, yarda da mutanen boye ko aljanu abu ne da ya zama ruwan dare, hakan ya sa ko yaya abu ya samu wani sai a ce shafar aljannu ce.

Ina cikin tafiya a hankali a kofar wani tsukakken shago mai cunkoson jama'a a yankin Himalaya na kasar India.

A wani kauye mai suna Bemni tare da mijina da kuma 'ya'yana biyu, a inda nake yin bincike akan sauye-sauyen da ake samu a tsakanin al'umma.

Kwatsam karen mai jiran shagon sai ya tasowa dana Finn dan shekaru hudu da haushi.

Shi dai karen aikinsa shi ne kula da dabbobin kauyen da daddare, dan kare su daga harin damisa.

Finn wanda ya fi karen tsaho ya yi matukar tsorata, nan take ya fara ihu.

A lokacin da nake rarrashin Finn, sai na ga mai shagon ya shige ciki, ya dawo tare da wata tsohuwa.

Ta zo da toka a hannunta ta na murzawa, sai idanun Finn suka bude a lokacin da ta fara zagaya kansa da tokar.

Sai ta fara karanta wani surkulle a hankali tare da tofa masa akan shi, nan da nan na gane abinda take yi, tana tunanin yana ihu ne saboda aljanu sun shafe shi.

A yanzu tana korar aljannun da suka hau kanshi ne, a hankali kuma sai Finn ya daina kukan.

Mai shagon sai ya kalle ni ya kada min kansa, wato yana nufin cewa an gama komai ya wuce.

Sai mutanen da suka yi dandazo suka yi shewar nuna jin dadi, mu kuma muka cigaba da tafiya.

Matsalar shafar aljannun babbar magana ce a Bemni.

Akwai lokutan da ake ganin aljanu ka iya shafar mutanen kauyen, misali a wajen biki, ko bukuwan addini.

To a nan ne aljanun iyaye da kakanni sukan shiga jikin mutum, yawanci a lokutan farin ciki, misali a lokacin da za a yi wa yarinya aure.

Image caption Yankin Himalayas yanki ne mai tsananin sanyi

Wanda aljanun suka shafa zai yi ta kuka, ko girgida kai, ko jijjiga kafada da dukan kirji.

Nan da nan kuma sai mai shafar aljanun ya dawo hayyacinsa ya cigaba da shagalin da ake na bikin, wanann na daga cikin al'adar kauyen.

Duk yaron da ya cika wasa ko yawan zama cikin yanayin bacin rai ana ganin shi ma aljanu ne suka shafe shi.

Iyaye sukan kira wani babba ko mai maganin gargajiya na Hindu ya zo dan ya cirewa yaron bakaken aljanun da suke kansa, irin wannan maganin yana daukar lokaci kafin yaron ya warware, kuma lokaci-lokaci yakan taso.

A wasu lokutan matasa na fakewa da shafar aljanu, misali sukan ce: ''na kasance mai hazaka a makaranta, daga baya sai aljanu suka shafe ni.''

Amma abinda ya fi damun mutanen kauye shi ne bakaken aljannun da ke bacewa a daji su shafi mutum.

Irin wadannan aljanu kan sa mutum ya yi ciwo, ko ma su kashe shi.

Shekaru hudu da suka gabata da yammacin lokacin sanyi Mohan Singh ya taba haduwa da irin wadannan bakaken aljanu.

Yana sarar itace a cikin daji, kwatsam sai wani mutum ya tunkaro inda ya ke tare da tambayarsa: ''Me ya sa kake sarar bishiyar nan?''

Sai Mohan ya ce nan da nan sai ya ga wani bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya kamar ya makance.

Sai fatalwar ta cakumi rigarsa.

Hannun fatalwar yana bangare daya na jikin Mohan amma 'yan yatsunta sun tabo daya bangaren.

Tsawon gashin fatalwar ya kai gwiwarsa, kuma kaurinsa ya kusan kaurin kafadar yaro.

A lokacin fatalwar ta yi ta sauyawa zuwa girma kala-kala, ciki har da girman kaza.

Mohan ya ga kamar yana fafutakar ceto rayuwarsa, amma daga baya dai fatalwar ta sake shi bayan da ta bace bat.

Mohan ya koma gida da matsanancin zazzabi.

Image caption Masu rawar addini

Ya kara da cewa ''Wannan fatalwa ta kama ni.''

Zazzabin nasa ya sauka ne bayan da wani malamin Hindu ya sanya ya yanka akuya.

Irin wannan ba kasafai yake faruwa ba, amma wani makocin mu ya ce ya taba ganin dila da kan mutum.

Wasu kuma sun ce sun ga macizai masu magana na gadin tukwanen gwal.

A bangare daya kuma shi kansa kauyen na samun kariyar aljanu saboda wuraren bautarsu, sannan dazuzzukan da suka zagaye kauyen na da hadari.

Idan wani ya je aiki cikin daji ya yi dare, sai hankalin mutane ya tashi su ce ya hadu da aljanu.

Mutane sun ce wadannan aljanu suna shafar wadanda suke jin tsoro ne, dalili kenan da suka nuna damuwa ga makomar matasansu.

Koma menene gaskiyar batun, Hausawa na cewa tsafi gaskiyar mai shi.

Karin bayani