Rikicin kungiyar gwamnoni ya kara dagulewa

Tambarin jam'iyyar PDP
Image caption Tambarin jam'iyyar PDP

A Najeriya, rikicin kungiyar gwamnonin kasar ya dauki sabon salo, inda gwamnan jihar Rivers Rotimi Amaechi ya umarci sauran gwamnoni su kauracewa taron da gwamnan jihar Pilato Jonah Jang ya kira.

Gwamna Jang wanda shi ma yake ikirarin shugabancin kungiyar ya kira taron ne a yau litinin.

Shi dai gwamnan na jihar Rivers ya kuma umarci gwamna Jonah Jang, da ya daina yi masa ungulu da kan-zabo, wajen ayyana kansa a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin kasar.

To sai dai wasu mukarraban gwamna Jang, sun ce ba- gudu- ba- ja- da- baya, sai an gudanar da taron gwamnonin.

Karin bayani