Ban san makoma ta ba —Tevez

Image caption Tevez ya ce bai san makomarsa ba

Dan wasan gaba na Manchester City, Carlos Tevez , ya ce bai san komai dangane da hasashen da ake yi cewa zai bar kulob din ba .

An dade ana jita-jitar cewa Tevez zai bar kulob din tun a karshen kakar wasanni ta bara, ana mai dangata shi da yiwuwar komawa Paris Saint-Germain, ko Juventus ko Monaco.

Sai dai dan wasan, mai shekaru 29 a duniya, ya dage cewa babu wani kulob da ya tuntube shi, kuma bai ma san makomarsa ba.

A cewarsa, ''A gaskiya ban san makoma ta ba. A halin yanzu ina hutu kuma babu wanda ya gaya min komai. Ina jira na ga abin da zai faru''.

A baya dai Tevez ya so komawa kulob din Boca Juniors, sai dai ya ce da wuya ya koma nan kusa.

Tevez ya bugawa wasanni sau 47 a gasar da City ta shiga a bara, kuma ya zura kwallaye 17.

Karin bayani