Najeriya na cigaba da tsare 'yan Kenya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Hukumomin Kenya sun ce sun bude kofofin diflomasiyya, domin tattaunawa da hukumomin Najeriya, saboda a sako wasu jami'an kasar ta Kenya da ake tsare da su a Lagos.

Jami'an da aka tsare din sun yi rakiya ne ga wani dan kasuwa dan asalin Najeriya, wanda hukumomin Kenya suka baiwa umarnin ficewa daga kasarsu.

Ko da yake yunkurin jin ta-bakin hukumomin Najeriyar ya ci tura, dan kasuwar da jami'an suka raka ya ce ba za a saki jami'an Kenyan ba har sai an kyale shi ya koma can.

Kafofin yada labarai na Kenya sun ambato sakatariyar harkokin wajen kasar, Amina Mohamed tana cewa hukumomin Najeriyar sun kasa fahimtar cewa jami'an Kenya basu kar zomon ba rataya aka basu.

Sai dai kuma ta ki yin cikakken bayani game da tabbacin da ta bayar cewa an bude kofofin diflomasiyya don tattaunawa a kan yadda za a kawo karshen al'amarin.

Jami'an Kenya

A cewar kafofin yada labaran na Kenya, kusan makwanni biyu ke nan da ake tsare da jami'an na rundunar 'yan sanda da hukumar shige-da-fice, da ma jirgin saman da suka yi shata a filin jirage sama na Murtala Muhammed dake Legas.

Jami'an sun sauka a Legas ne domin yin rakiya ga wasu 'yan Najeriya su biyar da aka kora daga Kenya, ciki har da wani dan kasuwa mai suna Anthony Chinedu, wanda ya kwashe shekaru biyu yana shari'a da matarsa 'yar asalin Kenya.

Hukumomin kasar ta Kenya dai na zargin Mista Chinedu da safarar miyagun kwayoyi; amma a cewar kafofin yada labaran, ya gamsar da hukumomin Najeriya cewa korarsa daga Kenya wata kutungwila ce ta damfararsa kudin da suka tasamma dalar Amurka miliyan shida.

Kawo yanzu hukumomin Najeriyar ba su ce komai ba game da dalilan cigaba da tsare jami'an Kenyan.

Shi kuwa kakakin ma'aikatar wajen kasar, Amadu Ogbole, shaida wa BBC cewa ba shi da labarin tsare mutanen.

Karbe Fasfo

Ga alama dai takardun tafiye-tafiyen jami'an Kenyan aka kwace, domin kuwa da wakilin BBC a Legas ya ziyarci otel din da 'yan Kenyan suke a wajen birnin, ya gansu suna watayawa abinsu, ko da yake sun ki ce masa komai.

Shi kuwa Mista Chinedu ya shaidawa wakilin na BBC cewa yana so ya koma Kenya, saboda ya baro 'ya'yansa da harkokin kasuwansa na miliyoyin daloli, baya ga wata shari'a a kotu.

Ya kuma yi barazanar cewa ba za a kyale jami'an na Kenya su koma gida ba, har sai an ba shi damar komawa.

Sai dai ya ki ya bayyana abin da ya dogara da shi yasa ya fadi hakan.

Kafofin yada labarai na kasar Kenya dai sun ambato sakatariyar harkokin, waje Amina Mohammed ita ma tana cewa yin karin bayani a kan wannan al'amari zai sa al'amura su kara rincabewa.