Yawan 'yan gudun hijira na karuwa

refugees
Image caption Wata 'yar gudun hijira a wani sansanin 'yan gudun hijira

Sabbin alkaluma da Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar sun nuna cewa, yawan mutanen da ke tserewa daga gidajensu ya kai yawan da bai taba kaiwa ba, tun lokacin rikicin Rwanda da na Bosnia.

A cewar shugaban Hukumar, Antonio Gutteres mutane fiye da miliyan bakwai ne suka rasa muhallinsu a bara, kuma adadin ya wuce fiye da yadda ake tunani.

Mista Gutteres yace rikicin Syria lamari ne dake sauya yadda al'amura suke, kuma yawan mutanen dake tserewa daga gidajensu daga Syria tun farkon shekarar nan kusan daya yake da sauran na sassan duniya.

'Yan gudun hijira da dama ne suka rasa muhallinsu a shekarun da suka gabata, duk da cewa an shafe tsawon shekaru tun bayan aukuwar rikicin Somalia da Afghanistan, kuma abin damuwa ne a ganin hukumar cewa, kasashen duniya sun gaza wajen hana wa ko shawo kan tashe- tashen hankula.

Bugu da kari yayin da kasashen Turai ke kara tsaurara dokokin shige da fice, galibin 'yan gudun hijira a yanzu na samun kulawa a kasashe ne masu tasowa dake da karamin karfi.