An hana amfani da wayar Thuraya a Borno

Birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya
Image caption Birnin Maiduguri na jihar Borno a Najeriya

Rundunar tsaro ta hadin guiwa ta JTF ta hana amfani da wayar tauraron dan adam ta Thuraya a jihar Borno, bayan harin da aka kai kan wata makaranta tare da kashe dalibai.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa dauke da sa hannun kakakin rundunar, Laftanal kanal Sagiru Musa.

Sanarwar ta ce an haramta amfani da wayar tauraron dan adam ta thuraya ne, saboda masu tada kayar baya na amfani da ita a matsayin kafar sadarwa dan shirya kai hare-hare.

Rundunar tsaron dai na zargin 'yan kungiyar Boko Haram sun yi amfani da wayar wajen kai hare-hare, a kan wasu makarantu biyu a jihohin Borno da Yobe, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dalibai akalla goma sha shida.

Haka kuma dokar ta hana sayar da katin wayar da kuma sayar da wayar dumgurumgun, kuma matakin zai fara aiki ne daga yau laraba a jihar Borno.

Sanarwar ta ce jami'an tsaro za su kama duk wanda suka gani da abin da ya shafi wayar.

Sai dai sanarwar ba ta ce komai ba game da cewa ko dokar za ta shafi 'yan jarida ko jami'an gwamnati da wadanda ke amfani da wayar a lokutan da suka kai ziyarar aiki jihar, da 'yan kungiyoyin aikin jin kai dake tallafa wa jama'a.

A ranar litinin din da ta gabata ne wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne, suka kai hari a kan wata makaranta a jihar Borno tare da hallaka dalibai tara da suke rubuta jarabawa.

Irin wannan harin ya faru a makociyar jihar wato Yobe, inda nan ma aka kashe wasu dalibai bakwai dake rubuta jarabawa da kuma malamai biyu.

Sojojin Najeriyar dai a baya sun yi ikirarin samun nasara a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram, a hare-haren da suka kaddamar musu, tun bayan ayyana dokar ta baci a jihohi uku dake yankin arewa maso gabashin kasar.