Majalisar Dinkin Duniya za ta ci gaba da aiki a Somalia

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Somalia, Nicholas Kay ya sheda wa BBC cewa Majalisar za ta ci gaba da gudanar da aiki a kasar duk da harin da 'yan gwagwarmayar Islama su ka kai ofishinta dake Mogadishu.

Ya ce ba su da aniyyar zuwa ko'ina, kuma Majalisar na da ikon kasancewa a Somalia.

Ma'aikatan Majalisar hudu aka kashe da masu gadi hudu da kuma wasu fararen hula.

Suma 'yan gwagwarmayar sun rasa mutanensu bakwai a harin na ranar Laraba.

A jiya ne masu kishin Islama suka kai hari a ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Mogadishu, babban birnin Somalia, kuma harin ya hallaka mutane akalla goma sha huɗu .

Ginin Majalisar Dinkin Duniya dake Mogadishu, babban birnin Somalia yana wuri ne tsattsauran tsaro a birnin.

Wanda ba shi da nisa da filin saukar jiragen saman ƙasar da aka killace da matakan tsaro sosai, kuma wuri ne da ke kusa da muhimman gine-ginen gwamnatin Somalia.

Sai dai kuma waɗanda suka kai harin sun kutsa ne, suka tsallake dukkan shingayen tsaro, har suka kai ga cikin ginin, inda suka tada bama-bamai.