An kaiwa Majalisar Dinkin Duniya hari

Hari a ofishin majalisar dinkin duniya a Mogadishu
Image caption Hari a ofishin majalisar dinkin duniya a Mogadishu

Masu fafutukar Musulunci a Somalia sun hallaka akalla mutane 14, a harin da suka kai wa harabar majalisar dinkin duniya a birnin Mogadishu.

Ministan harkokin cikin gidan Somaliyar ya ce, 8 daga cikin mamatan ma'aikatan majalisar ne, cikinsu har da 'yan kasashen waje 4.

Maharan sun tarwatsa kofofin shiga ginin majalisar dinkin duniyar, ta hanyar yin amfani da wata mota da ke makare da bama bamai.

Wani kakakin majalisar da ya shaida lamarin ya ce, ma'aikata a kidime sun buya a cikin wani rami na karkashin kasa mai cikakken tsaro, har zuwa lokacin da sojojin Somalia da na Tarayyar Afirka suka shawo kan lamarin..

Kungiyar al-Shabaab ta ce ita ta kai harin, inda mahara guda bakwai su ka hallaka.