Karzai ya ce zai tattauna da Amurka

Yanzu dai BBC ta fahimci cewa, Shugaba Hamid Karzai ya ce, a shirye yake ya ci gaba da tattaunawa da Amurka dangane da batun tsaro da tun farko ya sanar da cewar ya dakatar.

Wani kakakin shugaba Karzai ya ce, Sakataren hulda da kasashen wajen Amurka, John Kerry, ya yi magana da Shugaba Karzai ta waya akan wannan batu.

Kakakin shugaba Karzai ya kuma ce, John Kerry ya ce, kungiyar Taliban, wadda za ta bude ofis gobe a Qatar za ta cire tutarta da kuma tambarin Jamhuriyar Musulunci ta Afghanistan daga ofishin.

Sai dai kuma Muhammad Shaheen, kakakin kungiyar Tailiban ya fada wa BBC cewa, kungiyar Taliban tana da fatan cewa tattaunawar da za ta yi da Amurka za ta kawo wani ci gaba.

Ya ce kuma ce Taliban tana bukatar dukkan 'yan kasar Afghanistan, ba wai sai masu wakiltar bangaren gwamnati ba kawai.

A nasa bangaren dai, Shugaba Obama cewa ya yi da ma Amurka ta yi zaton za a samu sabani da gwamnatin Afghanistan, amma ya ce abu mafi muhimmanci shi ne sasantawa da masu tada kayar baya.