Rashin abinci mai gina jiki na illa ga tattalin arziki

hunger africa report
Image caption Wasu yara dake cin abinci a makaranta

Masu binciken sun yi nazari a kan kasar Uganda , inda suka ce rashin abinci mai gina jiki a farkon shekarun yara ya sa kasar ta yi asarar kusan kashi shida cikin dari na kudaden shigar da take samu.

Haka lamarin yake a wani bincike makamancin haka da aka yi a kan kasar Gautemala.

Hazakalika rahoton ya ce tamowa ta fi illa ne a lokacin da yara ke kanana inda yaran da basu samu abinci mai gina jiki ba kan kamu da cuttutuka kuma abu ne da ake kashewa kudi mai yawa domin samar masu da magani.

Masu binciken sunce yaran da basu samu abinci mai gina jiki da zai sa su girma cikin koshin lafiya, basu cika taka wani abin a zo a gani ba a makaranta, kuma iyayensu kan kashe kudi a kan kayan makaranta da kuma littafai.

Sai dai babar illar ita ce kan aiki inda biciken dai ya nuna cewa yaran da basu samu abinci mai gina jiki ba,idan sun girma ba su cika tasiri ba a wuraren ayyukansu kuma ba sa samun albashi iri daya da takwarorinsu da suka samu abinci mai gina jiki.

Wadanda da suka rubuta rahoton sun ce yawan kudaden da zaa kashe, domin ciyar da yara abinci mai gina jiki a dukanin wuraren da suka yi bincike, ya zuwa yanzu bai kai illar tattalin arzikin da za'a samu idan ba a yi haka ba