An dage shari'ar Kenyatta zuwa Nuwamba

Shugban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Image caption A watan Maris ne aka zabi Kenyatta a matsayin sabon shugaban kasar Kenya

Kotun hukunta manyan laifukan yaki ta duniya, ICC ta dage shari'ar shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta,wanda ake zargi da laifufukan cin zarafin Bil' adama.

Kotun ta ICC ta ce za'a fara sauraren karar ce a cikin watan Nuwamba mai zuwa, maimakon watan gobe kamar yadda aka tsara tun farko.

Lauyoyin Mr. Kenyatta ne dai suka nemi karin lokaci, domin shiryawa shari'ar.

Shugaban na Kenya da mataimakinsa, William Ruto, dukansu suna fuskantar shari'a a kotun ta ICC, bisa zargin kitsa tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar a shekarar 2007.

Ana sa ran fara shari'ar Mr. Ruto a cikin watan Satumba mai zuwa.

Kungiyar taryayyar Afrika ta nemi a dakatar da shari'ar, tana mai cewa ICC na farautar 'yan Afrika ne.