Keke mai tashi sama maganin cunkoso

Keke mai tashi sama
Image caption Keke mai tashi sama

Idan ka gaji da samun kanka a cunkoson ababen hawa, me zai hana ka tashi sama?

Wannan keken da ake ninke shi, wanda aka yiwa lakabi da Paravelo, keke ne kuma jigin sama.

Amma ba shi da saukin hawa kamar keke.

Wadanda suka kirkiro shi sun dage cewa za a iya kwance shi a shiga da shi cikin ofis kuma yana iya tashi sama da nisan kafa dubu hudu, gudunsa kuma ya kai mil 25 duk sa'a guda.

Har ila yau game da fasarar , an kirkiro wata safar kafa wacce kamfanin Heapsylon dake Amurka ya kirkira.

Safar dai na sa ido kan yadda mutum ke taka kasa wajen tafiya ko kuma idan yana gudu.

An tsara ta ne ta taimakawa masu tsere su kauce wa jin rauni.

Wani madauri dake idon sahu a safar na aikewa da bayanai ga wayar komai da ruwanka ko kwamfuta domin yin nazari.

Duk da cewa safar na dauke da na'urori ana iya wanke ta.