PDP ta rasa wasu 'ya'yanta

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya
Image caption Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya

A Najeriya, majalisar koli ta jam'iyyar PDP mai mulki ta amince da murabus din da wasu 'yan kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa suka yi.

Jami'an dai sun yi murabus ne a taron da jami'ar ta gudanar a yau, saboda hukumar zaben kasar ta ce ba a bi ka'ida wajen zabensu ba.

Jam'iyyar PDP ta ce nan gaba kadan za ta gudanar da babban taronta, don zaben wadanda za su maye gurbinsu.