Yau ce ranar 'yan gudun hijira

Image caption Wani sansanin 'yan gudun hijira a Kamaru

Yau ce ranar 'yan gudun Hijira ta duniya, kumafugees Majalisar dinkin duniya ce ta ware ranar ashirin ga watan Yunin kowacce shekara don faɗakar da jama'a game da wahalhalun da 'yan gudun hijira ke fuskanta.

A yankin Bosso dake gabashin jamhuriyar Nijar kimanin 'yan gudun Hijira dubu shidda ne hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD, UNHCR ta ce sun nemi mafaka, bayan da suka tsere ma tashin hankali tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar Boko Haram a wasu yankuna na Nijeriya.

Rikice-rikice a sassan duniya daban daban suna haddasa karuwar 'yan gudun hijira a sassa da dama na duniya.