Ana zaman ɗar-ɗar a yankin Shandam

Rahotanni daga Jihar Filato a Nijeriya, na cewa ɗimbin mutane na tserewa daga ƙauyukansu dake ƙaramar hukumar Shendam a kudancin jihar, sakamakon zaman ɗar-ɗar bayan sace shanun wasu Fulani makiyaya.

Wannan lamari na zuwa ne yayin da kura ke lafawa bayan wani jerin tashin hankali a ƙaramar hukumar Wase mai maƙwabtaka, wanda ya haddasa asarar rayuka.

Jihar Plateau ta yi ƙaurin suna wajen tashe tashen hankula masu nasaba da ƙabilanci da kuma addini.